Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta Eha-Amufu Babbar makarantar gwamnatin tarayya ce da ke Eha Amufu, Jihar Enugu, Najeriya.[1][2][3] Tana da dangantaka da Jami'ar Najeriya Nsukka dangane da shirye-shiryenta na digiri. Shugaban kwalejin na yanzu shine Pauline Ikwuegbu.[4][5][6][7]
Tarihi
An kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Eha-Amufu a shekarar 1981.[8]
An kafa kwalejin ne a ranar 21 ga watan Fabrairu, a shekarar 1981 a lokacin Gwamnan tsohuwar jihar Anambra na lokacin, Cif. Jim Ifeanyichukwu Nwobodo.[9] A ranar 23 ga watan Disamba na shekarar 1982, Majalisar Dokokin Jihar Anambra ta lokacin ta kafa wata doka ta sake kafa Kwalejin. An ambaci dokar a matsayin dokar jihar Anambra ta Najeriya mai lamba 28 ta shekarar 1982[10]wacce ta fara aiki a ranar 21 ga Fabrairu, shekarar 1981. A baya dai wurin ya kasance mallakin Kwalejin Horar da Malamai ta Gwamnatin Tarayya (TTC), Eha-Amufu.
Bayan sanarwar kafa Kwalejin Ilimi Eha-Amufu ta Gwamna daga ranar 21 ga Fabrairun shekarar 1981, an buɗe ofishin wucin gadi tare da 'yan tsirarun ma'aikatan a kusa da gidan talabijin na Anambra (ATV), Layout Independence. Enugu A ranar 7 ga watan Agusta, 1981, Kwamishinan Ilimi na Jihar Anambra na lokacin kuma Babban Sakatare na Ma'aikatar na lokacin ya kai sabon Provost da Registrar da aka nada zuwa wurin da kwalejin take a halin yanzu da ke Eha-Amufu kimanin kilomita 64 daga arewa maso gabas da garin makamashin kwal a Babban Birnin jihar Enugu. An fara rajistan na ɗalibai 196 a shekarar 1981 da ma'aikatan 147 wanda suka ƙunshi malaman koyarda ilimin malumta guda 23, Manyan Ma'aikatan Gudanarwa 15 da ƙananan ma'aikata 109[permanent dead link] . [11] An gudanar da bikin yaye daliban a shekarar 1984. Yawan ma'aikata a tsakanin 1981 - 1994 sun haɗa da ma'aikatan ilimi 89, gudanarwa 8, fasaha 58, ƙarami 231, jimlar 378. Tsakanin 1991-1994, jimillar ƙarfin ma'aikata ya kai 588 wanda ya kasance sakamakon faɗaɗawa a duk fannoni na Kwalejin ciki har da kayan more rayuwa.
Bayan kafa jiha a shekarar 1991, gwamnatin Jihar Enugu na wancan lokacin ta gaji kwalejin daga tsohuwar gwamnatin Jihar Anambra na lokacin. Kwalejin ta yi aiki a matsayin cibiyar jiha har sai da Gwamnatin Tarayya ta karbe ta a watan Afrilu, 1993 tare da gudanar da harkokin kudi daga Janairu, 1994. A doka mai lamba 4 na 1986 kamar yadda doka ta 34 ta 1993 da doka mai lamba 6 ta 1993 ta kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Eha-Amufu a tsakanin sauran kwalejoji 19. Don haka waɗannan Dokokin sun ba da duk tsarin da aka kafa a ƙarƙashin Dokar Jihar Anambra ta 1982.
Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Eha-Amufu ita ce Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta 20 a cikin tsarin kwalejojin ilimi na tarayya a Najeriya.