Kia Motors ( Korean , ki.a ) kamfanin motoci ne. Hedikwatar sa tana Seoul, Koriya ta Kudu. Shine kamfani na biyu mafi girman masana'antar kera motoci a ƙasar, bayan Kamfanin Hyundai. An sayar da Kia sama da 1.4 motocin miliyan a shekara ta 2010.[1] Kamfanin wani bangare ne na rukunin motoci na Hyundai Motor Group. Hyoung-Keun (Hank) Lee ya kasance shugaban kasa tun daga watan Agusta na shekarar 2009.[2]
Kalmar Kia ta fito ne daga kalmomin Koriya ma'ana "don tashi zuwa duniya daga Asiya".