Kande Balarabe

Kande Balarabe
Majalisar Wakilai (Najeriya)

Rayuwa
Haihuwa Saliyo
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a gwagwarmaya da ɗan siyasa

Sa'adatu Kande Balarabe 'yar siyasan Najeriya ce daga jihar Kano. Tana cikin mata uku da aka zaba a Majalisar Wakilan Najeriya a shekarar 1983. Ta yi aiki a wurare daban-daban a cikin jiharta ciki har da daraktar hukumar mata ta jihar Kano.

Rayuwa

An haifi Balarabe a Saliyo inda mahaifinta ke kasuwanci. Ta halarci makarantar mata ta Freetown da Royal School for Nursing a London. A 1982, a lokacin Jamhuriya ta biyu, Kande ta zama shugabar mata reshen mata na PRP a Kano. Kafin ta shiga siyasa, ta kasance ma’aikaciyar jinya a asibitin jihar, [1] mai suna asibitin Murtala Mohammed da ke Kano. Koyaya, a 1982, ta yi murabus don ta kashe mafi yawan lokacinta a siyasa. A cikin 1983, ta yi takara kuma ta sami kujera a Majalisar Wakilan Najeriya, amma, an yanke jamhuriya ta biyu. A shekarar 1987, ta zama mamba a majalisar wakilai, tana wakiltar wata gunduma a cikin jiharta sannan daga baya aka nada ta Darakta a Hukumar Mata ta Jihar Kano.

Manazarta

  1. Nelson, B. J., & Chowdhury, N. (1994). Women and politics worldwide. New Haven: Yale Univ. Press. P. 516