Kogin Kaduna,,da Turanci (River Kaduna) na da tsawon kilomita ɗari biyar da hamsin 550. Mafarinsa daga jihar Plateau, kilomita ashirin da tara 29, daga kudu a Jos, zuwa kogin Nijar a garin Muregi. Ya bi cikin birnin Kaduna, da wasu ungowani kamar su Kabala da kinkinau da kuma garuruwan, Zungeru da Wuya.