Joseph Nyumah Boakai, Sr (an haife shi a 30 ga Nuwamba, shekara ta alif ɗari tara da arba'in da hudu 1944A.c) ɗan siyasan Liberiya ne. Ya kasance Mataimakin Shugaban Laberiya tun daga Janairun 2006, yana aiki a ƙarƙashin Shugaba Ellen Johnson Sirleaf .
a shekarar 2016, Boakai ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Liberia a zaɓen shekarar 2017 . Mutane da yawa suna kallon sa a matsayin ɗan takara mai aminci da rashin tsari. Ya fafata da Sanata kuma tauraron kwallon kafa George Weah a zagaye na biyu, amma ya sha kashi a hannun Weah.[1][2]