Johnson Kwaku Adu (an haife shi a ranar goma 10 ga watan Agusta shekara ta, alif dubu daya da dari tara da sittin da tara 1969) ɗan siyasan Ghana ne kuma memba na majalisar dokoki ta bakwai na Jamhuriyyar Ghana ta huɗu kuma majalissar ta takwas 8 ta Jamhuriyyar Ghana ta huɗu, mai wakiltar mazabar Ahafo Ano ta Kudu maso yamma a yankin Ashanti akan tikitin. na New Patriotic Party.[1][2]
Rayuwar farko da ilimi
An haifi Adu a ranar goma 10 ga watan agusta a shekara ta, alif dubu daya da dari tara da sittin da tara 1969 a Akrokerri a cikin yankin Ashanti. Ya sami Diploma a Chemistry/ a shekara ta, dubu biyu 2000. Ya sami BEd (Science) a Jami'ar Ilimi, Winneba a shekarar, dubu biyu da daya 2001.[1]
Rayuwa ta sirri
Adu Kirista ne kuma abokin tarayya a Cocin Fentikos.[1] Yana da aure da ’ya’ya biyu.[3]
Aiki
Adu ya kasance kodinetan NADMO na gundumar Ahafo Ano ta kudu daga shekarar dubu biyu da biyu 2002 zuwa shekarar alif dubu biyu da tara 2009, da kuma ofishin kula da harkokin ilimi na Ghana (Circuit Supervisor) Ahafo Ano District Office daga shekarar, dubu biyu da goma 2010 zuwa shekarar alif dubu biyu da goma sha biyu 2012.[3] Sannan ya kasance malami mai koyar da kimiyya a Kwalejin Ilimi ta Akrokeri.[3]
Rayuwar siyasa
Adu dan jam'iyyar NPP ne.[4][5][6] Ya kasance dan majalisa mai rinjaye a majalisar dokoki ta 6 a jamhuriya ta hudu 4 ta Ghana. Ya kasance Shugaban Majalisar Wakilan Ahafo Ano ta Kudu, Mankraso, daga watan Afrilu shekara ta , dubu biyu da tara 2009 zuwa Janairu shekarar alif dubu biyu da goma sha ukku 2011; da MP daga watan Janairu shekara ta, dubu biyu da goma sha ukku 2013 zuwa yau; zangonsa na biyu kenan.[3]
Ya tsaya takara a babban zaben Ghana na shekarar, dubu biyu da ashirin 2020 akan tikitin New Patriotic Party kuma ya lashe zaben wakilci a majalisar wakilai ta takwas 8 na Jamhuriyyar Ghana ta hudu. Ya samu nasara da kuri’u dubu goma sha biyar da dari bakwai da sittin da daya 15,761 wanda ya samu kashi hamsin da hudu da digo hamsin da daya 54.51% na jimillar kuri’u yayin da dan takarar majalisar dokokin kasar NDC Sadik Abubakar ya samu kuri’u dubu goma sha ukku da dari da hamsin da ukku 13,153 ya samu kashi arba'in da biyar da digo arba'in da tara 45.49% na kuri’u da dan takara mai zaman kansa Adom Douglas Kwakye ya samu kuri’u dubu goma sha daya da hamsin da biyu 11,052.[7][8]
Adu shine shugaban kwamitin matasa, wasanni da al'adu[10] kuma memba a kwamitin lafiya.[11][12][13]
Rigima
A cikin watan Afrilun shekara ta, dubu biyu da ashirin da bakwai 2017, Hukumar Burtaniya a Ghana ta zargi Adu, George Boakye, Richard Acheampong, da Joseph Benhazin Dahah da taimakawa 'yan uwansu shiga Burtaniya ba bisa ka'ida ba ta hanyar amfani da fasfo din diflomasiyya. Adu ya tafi Landan ne tare da matarsa da diyarsa kuma ana zargin ya bar su a baya a Biritaniya.[14][15][16][17]