John Elliott, RIBA, (26 Oktoba 1936 - 13 Satumba 2010) wani masanin gine-ginen Biritaniya ne, mai tsara manyan otal-otal da wuraren shakatawa.[1] An haife shi a Portsmouth, Ingila, an san shi musamman saboda gudummawar da ya bayar a Gabas ta Tsakiya da kuma tsara, 7 star hotel, na Emirates Palace[2][3] a Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa.
Tarihin Rayuwa
Ilimi
John Elliott (Richard John Anthony Elliott), an haife shi a Portsmouth, Ingila. Bayan ya bar gida yana ɗan shekara 15, ya zagaya Turai kafin ya samu gurbin karatu a Makarantar Architectural Association School of Architecture [4] a Landan. Bayan kammala karatunsa, ya yi wani ƙaramin kwas a fannin ƙirar samfura a Makarantar Fasaha ta Tsakiya, [5] kafin sa mu tallafin gurabin karatu na gwamnatin, ya kammala karatun digirinsa na biyu a Cibiyar Fasaha ta Helsinki, Finland.
Farkon aiki
Bayan Finland ya koma Sweden inda ya shafe shekaru uku a ofishin Ralph Erskine. Shekarunsa a Sweden da Finland suna da tasiri mai zurfi a kan tsarinsa na tsara tsarin gine-gine, kuma wannan kwarewar ya Sa'a ka shi, fara mayar da hankali ga ƙira. A cikin shekara ta 1967, John ya zama babban mai tsara gari na farko na Abu Dhabi,[6] inda ya fara ƙwarewa a yankin Larabawa. Da farko yana da alaƙa da abubuwan farko na Abu Dhabi, John yana da alaƙa ta kud da kud tare da Sheikh Zayed bin Sultan Al Nahyan (1918 – 2004), mai mulkin Abu Dhabi kuma Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa (1971 – 2004).
Daga baya aikinsa ya kai shi ƙasar Saudiyya yana tsara ayyuka kamar a Jami’ar Sarki Abdulaziz da ke Jeddah da tuntubar al’ummar Jeddah da birnin Riyadh na gidan sarauta.
Sultan na Brunei
Baya ga gine-gine, John kuma ya yi aiki a na cikin gida da ake kira (interior design), a matsayin abokin gudanarwa na Dale Keller & Associates' Ofishin London. Anan, ya zana gidan sarauta mai girman murabba'in mita miliyan 3[7] wanda Sultan na Brunei ya ba da izini.
Hong Kong
Ya koma ofishin Dale Keller & Associate na Hong Kong, kuma ya shiga cikin sabbin otal da yawa a Kasar Sin da sauran sassan yankin Gabas. John ya zauna a Hong Kong na tsawon shekaru 13 kuma ya fara aiki tare da Wimberly Allison Tong & Goo 's[8] wanda ya kafa George J. "Pete" Wimberly.
WATG
A cikin 1991, John ya koma Burtaniya a matsayin memba wanda ya kafa kuma manajan darektan, Wimberly Allison Tong & Goo's (WATG) ofishin London. Ya zama memba na kwamitin gudanarwa kuma babban mataimakin shugaban ƙasa, wanda ya ƙware a ayyukan Gabas ta Tsakiya.
Rayuwa ta sirri
John Elliott yana da ƴaƴa huɗu, biyu daga aurensa na farko zuwa Lisbet Frolich, Timo da Maja, da yara biyu daga aurensa zuwa Erika Grohmann, Kelsey da Yolande. John da Erika sun girma Kelsey da Yolande a Hong Kong kafin su koma Birtaniya, inda suka zauna a Sandbanks, Dorset. Shekaru biyu bayan haka suka koma gidansu na Art Deco a shekarar 1930 a Landan, wanda John ya kwashe shekaru da yawa, yana sauya fasalin gidan.[9]
Kammalallun ayyuka
Gine-gine
Emirates Palace, Abu Dhabi, United Arab Emirates
Royal Mirage Daya&Kawai, Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa
Hilton 2000, Ras Al Khaimah, United Arab Emirates
The World Resort, Dubai, United Arab Emirates
Wurin shakatawa na Virgin safari, Masai Mara, Kenya
Mövenpick Hotels & Resorts Dead Sea Resort & Spa, Jordan
Jumeirah Beach Residence, Dubai, United Arab Emirates
Masu zaman kansu Palaces, Al Ain, United Arab Emirates
Shangri-La Hotels and Resorts Resort, Oman, Muscat
Sheraton Hotels and Resorts Abu Soma, Soma Bay, Egypt
Mövenpick Hotels & Resorts El Gouna, Misira
InterContinental Hotel Amman, Amman, Jordan
Grand Hyatt Amman, Amman, Jordan
Aqaba Beach Resort, Aqaba, Jordan
Marina Village Ayla Oasis Resort, Aqaba, Jordan
Legoland, Windsor, Birtaniya
Denia Marriott La Sella Golf Resort & Spa, Denia, Spain
Hyatt Regency La Manga Golf Resort, Spain
Hilton International Resort, Mauritius
Gallen, Switzerland
Asibitin Soja, Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa
Asibitocin kasa guda uku, Abu Dhabi, United Arab Emirates