John AW Bird (6 Fabrairu 1926 - 18 Nuwamba 1997).[1] ɗan siyasa ne a Biritaniya wanda ya rike matsayin Memba na Majalisar Tarayyar Turai (MEP).
Ƙuruciya
An haife shi a Wolverhampton, Bird ya sami horo a matsayin injiniya. Yayi aikin sojan kasa tare da dakarun sojojin Burtaniya a lokacin yakin duniya na biyu, sannan ya koya a Wolverhampton Polytechnic.
Siyasa
Bird ya kasance ɗan ƙungiyar kasuwanci na tsawon lokaci.[ana buƙatar hujja]A matsayinsa na shugaban Council, ya jagoranci karɓo kuɗaɗen Wolverhampton Wanderers FC a shekarar 1986.[2][3]
An zaɓi Bird zuwa Majalisar Tarayyar Turai a zaben fidda gwani na 1987, don wakiltar mazabar Midlands West.[4]
Manazarta
- ↑ "3rd parliamentary term - John A.W. BIRD - MEPs - European Parliament". www.europarl.europa.eu.
- ↑ "From the archive - Wolves' financial peril 30 years on". www.expressandstar.com.
- ↑ "Wolves SOLD: It's been 30 years of growth". www.expressandstar.com.
- ↑ "Malta". Department of Information. 20 May 1988 – via Google Books.