Jami'ar Aikin Noma ta Michael Okpara, asali ita ce Jami'ar Aikin Gona ta Tarayya, jami'a ce ta tarayya a Umudike, Jihar Abia, Najeriya an kafa ta a matsayin Jami'ar musamman ta Gwamnatin Tarayya ta Najeriya Dokar No 48 na Nuwamba shekara ta 1992. Ta fara ayyuka na yau da kullum a watan Mayu shekara ta 1993 tare da naɗin Majalisar farko da Mataimakin Shugaban Jami'ar Farfesa Placid C. Njoku a ranar 27 ga Mayu shekara ta 1993, yayin da aka nada wasu manyan jami'an Jami'ar daga baya.
An shigar da rukunin farko na ɗaliban a cikin makarantar a cikin shekarar ilimi ta 1993/94 tare da yawan ɗalibai 82.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Manazarta