Jalingo ita ce babbar birnin jihar Taraba (a da tana ƙarƙashin Jihar Gongola ne), kuma ita ce cibiyar gwamnatin jihar. Mafiya yawan al'umman dake zaune a garin Jalingo Fulani ne. Amma akwai Kuteb, Hausawa da wasu yararrukan dake zaune a garin suna gudanar da harkokinsu, an kiyasta adadin al'umman birnin sunkai dubu dari da goma sha takwas (118,000). Garin Jalingo yana a tsakiyar duwatsu ne. Jalingo tana da masarauta da sarakunan yanki. Masarautar ta samo asali ne daga Musarautar Muri.[1][2][3][4][5][6][7][8]
Ilimi.
A cikin garin Jalingo, akwai makarantun daban-daban masu tarin yawa kama daga firamari, sakandari har ma da Jami'o'i na Ilimi da Likitanci; wanda wasu na gwamnati (government), ne wasu kuma mallakan Anguwa ne (community), wasu kuma mallakan mutane ne (private).
Daga cikin makarantun firamari mallakan gwamnati akwai irin:
Bugu da kari, akwai Jami'a guda daya a cikin garin: Taraba State University Jalingo, wacce ake kira da TSU.[26]
KASUWANNI.
Ƙaramar hukumar Jalingo a kasancewar ta fadar Jiha. tana da kasuwanni a cikin ta masu tarin albarka, wanda ake saye da sayarwa. Daga cikin wadannan kasuwanni akwai: