Shiekh Ja'afar Mahmud Adam (Fabrairu 12, 1960 - Afrilu 13, 2007) ya kasance masanin addinin Salafiyyah kuma memba na Jama'at Izalat al Bid'a Wa Iqamatus Sunnah na Najeriya, ƙungiyar addini da siyasa da ke da hedikwata a Abuja . Ya zaun a Kano kuma yana tafiya Maiduguri don Ramadan Tafsir na shekara-shekara.[2]
Mutuwarsa
An kashe Sheikh Ja'afar a masallacinsa yayin sallar Subh a arewacin birnin Kano a watan Afrilu na shekara ta 2007. Ra'ayoyi sun rabu a wannan lokacin game da wadanda suka aikata laifin. Duk da yake wasu sun ce Boko Haram, wata kungiya mai tsattsauran ra'ayi, ta kashe Sheikh din, wasu sun ce Mista Shekarau, gwamnan Kano a lokacin, na iya kasancewa da alhakin saboda malamin yana daya daga cikin manyan masu sukar sa.[3]
Abu Musab Al-Barnawi ɗan shugaban Boko Haram)">Mohammed Yusuf, wanda ya kafa Boko Haram, a cikin littafinsa na 2018, Abu Musab al-Barnaui - Slicing off the Tumor Book - Yuni 2018 ya tabbatar da cewa Jafar Adam ya kashe shi da kanaan Taliban, wanda aka fi sani da Taliban na Najeriya [4][5]
Bayanan da aka ambata