Wing Commander (ritaya) Isa Mohammed an naɗa shi gwamnan soji a jihar Gongola taNajeriya daga watan Disambar shekara ta 1987 zuwa Disambar shekara ta 1989 a lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida.[1]
A matsayinsa na gwamna, bisa umarnin Babangida na biyu, Vice Admiral Augustus Aikhomu, ya ki miƙa ma’aikatan ofishin ga Hakimin Kilba na karamar hukumar Hong a Gongola. A lokacin da wata kotu ta yanke hukunci kan wasu mutane biyu da ke neman shugabancin kananan hukumomi bisa dalilan rashin bin ka’ida a zaɓen, Isa Mohammed ya ki amincewa da hukuncin ya rantsar da su a matsayin shugabannin. Ya kai karar kungiyar lauyoyin Najeriya a lokacin da suka kauracewa kotunan domin nuna rashin amincewarsu, sannan kuma ya shigar da ƙarar Punch a kan yadda ta kai rahoton lamarin.[2][3]
Bayan ya yi ritaya ya zauna a unguwar Rayfield da ke garin Josa Jihar Filato . A cikin watan Afrilun shekarar 2006 yana cikin wasu da aka gurfanar da shi a gaban kuliya bisa laifin tafiyar da ƙungiyar Turaki Vanguard, ƙungiyar da ke biyayya ga mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, wadda gwamnati ta yi ikirarin haramtacciyar ƙungiya ce.[4][5]