Ibrahim Sharukhan

Ibrahim Sharukhan jarumi ne a masana'antar fim ta hausa wato Kannywood, ya jima a masana'antar ,Yana fitowa a matsayin jarumi, Yana Hawa Wakokin yabon Manzan Allah, Yana sanƙira na biki ko suna ko wani taro na farin ciki. Sannan Kuma furodusa ne mai shirya finafinai.[1]

Takaitaccen Tarihin Sa

Mc Malam Ibrahim sharukhan gidan biki, saboda son da yake ma fina finan indiya yasa ake masa inkiya da sharukhan. Haifaaffen Karamar hukumar wudil ne a jihar Kano, yayi karatun firamare da sakandiri a garin Kano. ya fara da zama jarumi ne daga baya ya koma furodusa daga Nan ya zama Mai shirya fina finai, daga Nan ya zama mc na Taron biki, inda har ya mallakin katin Santa na taro Mai suna "gidan biki event center". Jarumin yayi aure Yana da mata daya da yaro namiji guda daya Mai suna muhammad sajeed.[2][3]

Manazarta