Ibrahim Kunle Olanrewaju ɗan siyasan Najeriya ne. Ya kasance memba mai wakiltar mazaɓar Ido/Osi/Moba/Ilejemeje a majalisar wakilai. [1]
Rayuwar farko da aikin siyasa
Ibrahim Kunle Olanrewaju ya fito ne daga jihar Ekiti. A shekarar 2019, an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar APC. A cikin shekara ta 2023, an naɗa shi a matsayin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Al'amuran Majalisar Tarayya (Majalisar Wakilai). [2][3]