Dr. Ibrahim Aminu Kurami An haifi shi a Kurami dake karamar hukumar Bakori ta Jihar Katsina. Ya rasu ranar 10 ga watan Oktoba, 2022 a Saudiyya.[1] Shi Likita ne kuma ɗan siyasa wanda yayi aiki a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina a tarayyar Nijeriya[2]
Farkon rayuwa da Karatu
An haifi Kurami a kauyen Kurami kuma ya fito daga babban gida ne,[3] a Ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina
Ya yi karatu a makarantar Sardaunan Memorial College, Kaduna a matsayin karatun secondary ko gaba da firamare. Daga nan ya tafi jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya inda ya karanci likitanci.[4]
Aiki da Siyasa
Kafin ya shiga harkar siyasa, Kurami ya kasance likita ne kuma, shi tsohon manajan darakta ne na kamfanin Macce investment Limited. An zaɓe shi a matsayin wanda zai yi takarar zama ɗan majalisa mai wakiltar Bakori a wani zaɓen da akayi na cikin jam'iyyar tasu ta APC ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 2020 domin maye gurbin wanda ya bar kujerar Alhaji Abdulrazaq Isma'il Tsiga,[5] Wanda ya rasu a watan Mayun 2020.[6]
Ibrahim Kurami yayi nasarar lashe zaɓen ɗan majalisar mai wakiltar Bakori biyo bayan samun ƙuri'u 20,444, wanda hakan yasa ya doke abokin hamayyar sa na jam'iyyar PDP Aminu Magaji wanda ya samu ƙuri'u 11,356 a zaɓen.
Iyali
Ibrahim Kurami yana da mata guda biyu, ƴaƴa 11 da kuma jikoki guda ukku.[1][2][4]
Mutuwa
An sanar da rasuwar Dakta Ibrahim Kurami ranar 10 ga watan Oktoban 2022 wajen ƙarfe 2 na dare, bayan gajeruwar rashin lafiya a birnin Madina, dake Saudiyya. Inda yaje domin aikin umara.[7]
Ya rasu shekara biyu bayan an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dokoki. An binne shi a birnin Madina.[8]