Hukumar zirga-zirgar ababen hawa ta kanohukuma ce ta gwamnatin jihar Kano wacce aka kafa ta don sauya tsarin sufurin jihar da tabbatar da tsarin zirga-zirgar ababen hawa a cikin jihar Kano tare da rage hatsarurruka akan hanya.[1][2][3][4]
Tarihi
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA) ko (AR5) hukuma ce ta kula da zirga-zirgar ababen hawa wacce tsohon GwamnanJihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya kafa a shekara ta 2012 domin tsabtace hanyoyin ta hanyar tabbatar da masu amfani da hanyoyi a cikin jihar ta Kano sun bi doka.[5][6][7][8]