Hennric David Yeboah (An haife shi a shekara ta alif dari tara da hamsin da bakwai (1957) - Ya mutu 1 ga watan Maris, shekara ta dubu biyu da sha tara(2019)[1][2][3] ɗan kasuwa ne[4][5] kuma ɗan siyasar Ghana na Jamhuriyar Ghana.[4][5] Ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Afigya Sekyere ta gabas na yankin Ashanti na Ghana a majalisar dokoki ta hudu 4, biyar 5, da shida 6 a jamhuriya ta hudu ta Ghana.[6][7] Ya kasance memba na New Patriotic Party.[4][5]
Rayuwar farko da ilimi
An haifi Yeboah a ranar goma sha daya 11 ga watan Maris shekarar alif dubu daya da dari tara da hamsin da bakwai 1957.[4][5] Ya fito ne daga Agona, wani gari a yankin Ashanti na Ghana.[4][5] Ya yi karatu a Malcolm X College a Chicago, Illinois. Ya sami digiri a cikin shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da shida 1986 daga kwalejin da aka ce.[4][5][8]
Aiki
Yeboah dan kasuwa ne kuma shi ne Shugaban Kamfanin Daphelia Enterprise Limited a titin Spintex a Accra, Ghana.[4][5][9]
Aikin siyasa
Yeboah ya kasance memba na New Patriotic Party.[4][5] Ya fara shiga majalisar ne a shekarar alif dubu biyu da hudu 2004 kuma ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Afigya Sekyere ta Gabas a yankin Ashanti na kasar Ghana.[4] Ya sake tsayawa takara karo na biyu a majalisar dokoki ta biyar 5 da ta shida 6 ta jamhuriya ta hudu.[6][7][10] A cikin shekarar alif dubu biyu da goma sha biyar 2015, ya yi rashin nasara a zaben fidda gwani na New Patriotic Party a hannun Mavis Nkansah Boadu.[11]
Zabe
An zabi Yeboah a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Afigya Sekyere ta Gabas na yankin Ashanti na Ghana a karon farko a babban zaben Ghana na shekara ta alif dubu biyu da hudu 2004.[6][10] Ya yi nasara akan tikitin New Patriotic Party.[6][10] Mazabarsa wani bangare ne na kujeru talatin da shida 36 na 'yan majalisa daga cikin kujeru talatin da tara 39 da sabuwar jam'iyyar Patriotic Party ta lashe a wancan zaben na yankin Ashanti.[12] New Patriotic Party ta samu rinjayen kujeru dari da ashirin da takwas 128 na 'yan majalisa daga cikin kujeru dari biyu da talatin 230.[13] An zabe shi da kuri'u guda dubu talatin da biyu da dari daya da arba'in da ukku 32,143 daga cikin dubu arba'in da daya da dari biyu da ashirin 41,220 masu inganci da aka jefa kwatankwacin kashi saba'in da takwas 78% na yawan kuri'un da aka kada.[6][10] An zabe shi a kan Edward Kusi Ayarkwah na National Democratic Congress, Adamu Alhassan na jam'iyyar Convention People's Party da Alhaji Amidu Adam na jam'iyyar Democratic People's Party.[6][10] Wadannan sun samu kashi ashirin da digo biyar 20.5%, kashi daya 1% da kashi sifili da digi sittin 0.60% bi da bi na jimlar kuri'un da aka kada.[6][10]
A shekarar 2008, ya lashe zaben gama gari a kan tikitin New Patriotic Party na wannan mazaba.[7][14] Mazabarsa tana cikin kujeru 34 na 'yan majalisa daga cikin kujeru 39 da New Patriotic Party ta lashe a wancan zaben na yankin Ashanti.[15] New Patriotic Party ta lashe kujerun 'yan majalisa dari da tara 109 daga cikin kujeru dari biyu da talatin 230.[16] An zabe shi da kuri'u dubu talatin da ukku da tamanin 33,080 daga cikin dubu arba'in da ukku da dari biyar da biyar 43,505 masu inganci da aka jefa kwatankwacin kashi 76.04% na yawan kuri'un da aka kada.[7][14] An zabe shi a kan Edward Ayarkwah na National Democratic Congress, Osman Isshak na People's National Convention, Amidu Alhaji Adam na Democratic People's Party da Obeng Nyantakyi Clement na Convention People's Party.[7][14] Wadannan sun samu kashi ashirin da daya da digo dittin da daya 21.61%, 0.59%, 0.29% da 1.47% bi da bi na jimillar kuri'un da aka kada.[7][14]
Rayuwa ta sirri
Yeboah Kirista ne.[4][5] Ya kasance memba na Cocin Kirista na Charismatic.[5] Ya yi aure da ‘ya’ya biyar.[5][17]
Mutuwa
Yeboah ya mutu a ranar 1 ga Maris, 2019, yana da shekaru 62 a duniya, yana karbar magani a asibitin koyarwa na Komfo Anokye da ke Kumasi.[1][8][18][19][20]
↑ 6.06.16.26.36.46.56.6Elections 2004; Ghana's Parliamentary and Presidential Elections. Accra: Electoral Commission of Ghana; Friedrich Ebert Stiftung. 2005. p. 117.
↑ 7.07.17.27.37.47.5Ghana Elections 2008. Ghana: Friedrich Ebert Stiftung. 2010. p. 57.