Hasumiyar Civic Tower, wadda kuma ake kira Civic Center Towers, Civic Towers, ginin ofishi ne mai hawa 16 a Legas (wasu majiyoyin sun ce hawa 15). hasumiyar na da ɗan tazara daga Civic Center akan hanyar Ozumba Mbadiwe Avenue, Victoria Island, Legas. An buɗe shi a hukumance a cikin 2015 kuma mallakar Business Tycoon Uzor Christopher ne.[1][2][3]
A ranar 20 ga watan Yuli, 2018, Gine-ginen Civic Towers da Civic Center sun haskaka da ja don bikin cika shekaru 50 na gasar Olympics ta musamman tare da fitattun wurare 225 a faɗin duniya.[4]
Manazarta