A ranar biyar 5 ga watan Yulin shekara ta dubu biyu da goma Sha biyar 2015, an kai wasu hare-hare a Najeriya - a Potiskum, Jos da Borno.
An kai hari a;
Potiskum
Da misalin karfe 10 na safe ranar 5 ga watan Yulin 2015, a Potiskum, jihar Yobe, an kai harin kuna baƙin wake a wata cocin Evangelical, Cocin Redeemed Christian Church of God.[1][2][3] Harin ya kashe mutane shida ciki har da maharin.[1][2][3]
Jos
Da yammacin wannan rana ne a birnin Jos na jihar Filato wani bam da aka dasa a wani gidan abinci ya fashe inda mutane 23 suka mutu.[4][3] A maraicen wannan rana a birni, an kai harin ƙuna baƙin wake a wani masallaci, wanda ya kashe mutane 21. [4] [3]
Borno
A dai ranar kuma amman a jihar Borno wasu gungun ‘yan tada ƙayar baya sun kashe wasu ƙauyawa 9, tare da ƙona majami’u 32 da gidaje kusan 300. [3]
Manazarta