Hari a MainokIri |
rikici |
---|
Kwanan watan |
25 ga Afirilu, 2021 |
---|
|
|
|
Wuri |
Mainok (en) |
---|
Ƙasa |
Najeriya |
---|
|
|
|
Adadin waÉ—anda suka rasu |
33 |
---|
A ranar 25 ga watan Afrilun 2021, wasu gungun ƴan ta'addar ƙungiyar ISWAP sun kashe sojoji 33 a Mainok, wani gari mai nisan mil 36 (kilomita 58) yamma da birnin Maiduguri a jihar Borno, Najeriya.[1][2]
Harin Ta'addancin
Mayaƙan Sanye da kayan soji, sun iso ne a cikin manyan motoci guda huɗu masu jure wa nakiyoyi, da harbi har wayau motocin masu sulke, sai kuma manyan motocin bindiga da dama. Sun rabu gida uku kafin su kai hari sansanin sojojin. ISWAP sun lalata tankin yaki na T-55, BTR-4EN, kuma ta sace MRAPs da yawa.[3][4][5] Maharan sun tsere zuwa sansaninsu da ke kewaye da layin Lawan Mainari, yayin da sojojin saman suka kai musu farmaki ta sama.[2][6] A lokacin da ‘yan ta’addan ISWAP suka yi arangama da jiragen soji da suka nufi wajensu domin kai musu hari, a fusace suka kona ofishin ‘yan sanda da ke Mainok sannan suka tsere zuwa makarantar firamare da ke can.[7]
Lokacin da sojoji suka iso daga Damaturu don mayar da martani, ISWAP sun yi wa sojojin kwanton bauna, inda suka kashe uku, suka raunata tara, sannan suka sace MRAP.[6] Wani jirgi marar matuki ya kai harin bam da gangan kan wata motar sojoji inda ya kashe mutane 20.[8][6]
Bayan faÉ—an
An kai harin ne aka É—auki tsawon lokaci ana gwabza faÉ—a a garuruwan Geidam, Kumuya da Buni Gari da ke lardin Yobe. Hukumar NAF ta tura intelligence, Surveillance and Reconnaissarce (ISR) inda aka girke su a sararin sama.[7]
Duba kuma
- Lokacin rikicin Boko Haram
- Jerin abubuwan ta'addanci a 2021
Manazarta