Hala El Badry (an haife ta a shekara ta 1954 a birnin Alkahira), wanda ta kammala karatun digiri a jami'ar Alkahira, 'yar jarida ce kuma marubuci 'yar ƙasar Masar. Ita ce mataimakiyar editan gidan rediyo da talabijin ta Masar.
Muntaha, wani littafi da aka buga a cikin shekarar 1995, an saita shi a ƙauyen almara na Muntaha a cikin Kogin Nilu. Imra'atun ma (Watacce Mace), Littafin Hala El Badry na huɗu, an naɗa shi mafi kyawun labari na shekara ta 2001 a Baje kolin Littattafai na Duniya na Alkahira .
Ayyuka
- Muntaha . 1995
- Muntaha . Nancy Roberts ta Fassara. Alkahira: Jami'ar Amurka a Alkahira Press, 2006. Shafukan da aka zaɓa
- Imra'atun ma . 2001