8W45+Q25, 771104, Lawanti, Gombe da Lawanti, Bauchi road
Sani Abacha International Airport ( filin jirgin sama ne da ke aiki a Gombe babban birnin jihar Gombe taNajeriya. An gina shi ne a kan hanyar Bauchi zuwa Gombe ta kauyen Lawanti da ke karamar hukumar Akko, Gombe. An fara shirin ne a cikin 2005 kuma an ba da takardar shedar tashi sama a 2008, jirgin farko na kasa da kasa zuwa Jeddah, Saudi Arabia. Filin jirgin saman Gombe na iya daukar jiragen dakon kaya, filin jirgin saman Gombe Lawanti yana da tsawon kilomita 3.5 kuma yana iya daukar jiragen dakon kaya a lokaci guda. Filin jirgin saman yana da cikakkun kayan aiki na zamani kuma yana da tsaro kuma yana da aminci ga tafiye-tafiye na gida da waje..