Garba Ibrahim Muhammad

Mukala mai kyau
Garba Ibrahim Muhammad
Hon. Garba Ibrahim Muhammad (Garba ÆŠiso)
Haihuwa (1958-05-24) 24 Mayu 1958 (shekaru 66)
Kano
Gurin zama Diso Qtrs, Gwale L.G.A. Kano
Kasar asali Najeriya
Makaranta Lycee Technique Du Hainaut Valenciennes France
Fara mulki 2015
Gama mulki To date
Notable work Free Integrated Maternal and Child Health Care Bill 2016
Office Nigerian House of representative
Karaga 2-term
Jam'iyyar siyasa New Nigerian People's Party (NNPP)
Yara 7
Iyayes Late Alƙalin Dawakin Kudu Alhaji Ibrahim Muhammad (father)
Hajiya Asma'u (mother)
Honours
  • Medaille de la Francophanie by the francophone Foreign Missions in Nigeria, in March 2015.
  • Knight of the French Order of the Academic Palms by the French Government, in November 2015.

Garba Ibrahim Muhammad: wanda aka fi sani da Garba Ɗiso (Ɗan Kano ne kuma ƙwararren injiniya ne a Nijeriya) An haife shi a ranar 12 ga watan Yuni, 1958). Shi ne shugaban kwamitin tsaro na cikin Majalisar Wakilan Nijeriya a yanzu. Ya kasance ɗan jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Gwale[1] a Jihar Kano a majalisar Wakilai ta tarayyar Nijeriya.

Rayuwar farko da ilimi

An haifeshi ne a ranar 12 ga watan Yuni 1958 a cikin garin Kano. A karo na farko an zaɓi Hon. Garba a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwale a Jihar Kano, a Jam'iyyar APC a shekarar 2015-2019. An ƙara zaɓar sa karo na Biyu a shekarar 2023.

Garba Ɗiso ya yi Firamare a makarantar Masallaci Special Primary school, a shekarar 1965 zuwa 1971, daga nan ya cigaba da karatun sa na sakandare a makarantar koyon fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire wadda aka fi sani da Government Technical College Wudil (G.T.C) Kano, a shekarar 1971 zuwa 1977, lokacin ana kiranta da Government Secondary Technical school (G.S.T.S) Wudil.

Ya Tsallaka ƙasar Faransa ya sami Diploma a fannin harshen Faransanci, a Cibiyar Audiovisuel des Langues Modernes, Vichy, Faransa. Ya yi digirinsa na farko a fannin lnjiniyancin Motoci a Jami’ar Lycee Technique Nationalise, Saumur France a shekarar 1978 zuwa 1981,[2] ya sami shaidar kammala B.T.S a makarantar Lycee Technique Du Hainaut Valenciennes France. A fannin Automobile Engineering/management wato Injiniyancin Tsare-tsare na ƙirƙirar motoci a faɗin duniya, a shekarar 1984.

Ya gudanar da hidimar ƙasa (NYSC) ne a 1985, a kamfanin peugeot da ke garin Kaduna. Saboda ƙoƙarinsa suka ba shi aiki a matsayin mai bada shawara a cikin kamfanin har tsawon shekara 7.

Garba Ibrahim Muhammad

Ya bar kaduna, a shekar 1991 ya shiga kamfanin Steyr da ke garin Bauchi, ya riƙe muƙamin Shugaban cinikayya da saye da sayasarwa na kamfanin tsawon shekara 7. Daga baya ya dawo gida kano don shirin shiga fagen siyasa a sheka ta1997.

Siyasa

Mutum ne mai himma da ƙwazo, bayan gwagwarmaya da aiki da ya yi a sassa daban-daban na Jahohin Nijeriya, ya shiga siyasa kai-tsaye bayan ya kammala karatunsa, a inda a shekarar 2011 zuwa 2012, an naɗa Garba Ɗiso a matsayin Kwamishinan kimiyya da Fasaha, daga baya ya zama Kwamishina mai Kula da Ayyuka da Kimantawa a shekarar 2012 zuwa 2014, duka a ƙarƙashin Gwamnatin Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso.

An fara zaɓar Ɗiso, a matsayin ɗan majalisa mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Gwale ta Jihar Kano Najeriya a ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Inda ya zama zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilai a ƙarƙashin Jam’iyyar APC a shekarar 2015-2019, a karo na biyu. Kuma a shekarar 2023[3] ya sake komawa kan kujerarsa ta majalisar a ƙarƙashin jam'iyar NNPP[4]. Ya kasance ɗaya daga cikin ƴan sahun gaba-gaba waɗanda suka goyi bayan Engr. Rabiu Musa Kwankwaso tun daga shekarar 1999.

Yana É—aya daga cikin 'yan majalisar Wakilai ta tarayyar Nijeriya masu Jin yaruka daban-daban kama daga, Hausa, Turanci da kuma Faransanci.

Kawo yanzu ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Wakilai ta tarayyar Nijeriya Tajudeen Abbas. An naɗa shi matsayin shugaban kwamitin tsaro na Majalisar a 2023.

Kwamitoci

  • Shugaban: Nigeria-France

Parliamentary Friendship Group.

  • Mataimakin shugaban: Freedom of

Information (FOI)

Kwamitocin Majalisa

  • Man fetur
  • Harkokin cikin gida
  • Public Procurement
  • Kimiyya da fasaha
  • Harkokin Gidaje
  • Ƙarafa
  • SDG

Darajoji

• Medaille de la Francophanie ta Ofishin Jakadancin Faransanci na Ƙasashen waje a Najeriya, a cikin Maris 2015.

• Knight of the French Order of the Academic Palms by the French Government in November 2015, Government, in November 2015.

Kuma sake dubawa

Manazarta