Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
.
Gandun Dabbobi na Bala A. Funtua fassarar shahararren littafin nan ne
mai suna Animal Farm, wallafar wani
baturen Ingila wanda ake kira George
Orwel, ko da yake dai sunansa na
gaskiya shi ne Eric Blair. Gandun
Dabbobi dai shagube ne, waton gugar
zana akan juyin mulkin da akayi a
ƙasar Rasha, a shekarar 1917 – wanda
akayi amfani da dabbobin da ake kiwo
a gandu domin isar da sako. Wannan
littafi ne mai manufar jigon
ilmantarwa, nishadantarwa da wayar
da kai ta hanyar zambo da kuma
farfaganda. Gandun dabbobi littafine
mai dauke da hikima da hangen nesa.
Labarin Littafi
Wadannan dabbobi sune suka taru a
karkashin wani tsohon alade waishi
Dattijo (Old Major) , don yayi musu
bayani na wani irin mafarki da yayi,
da kuma yanda zasu kori Nomau (Mr.
Jones) daga gonarsa don ta zama tasu.
Daga karshe dai sunci nasara wajen
korar Nomau daga gandu ta hanyar
tawaye (revolution) , kuma gandu ya
koma nasu, ya zama sune wuka sune
nama, bayan mutuwar Dattijo, wanda
ya mutu kwana ukku bayan
jawabinsa.
Kokarin marubucin
Marubucin yayi amfani da
aladu a matsayin dabbobi masu kaifin
tunani kuma masu iya tafiyar da
ragamar mulkin gandu, Musamman
Dantulu (Snowball) , Maitumbi
(Napoleon) , da Karambana (Squealer) –
Sauran dabbobi sun hada da su Aura
(Benjamin) , Akawal (Boxer), Godi
(Clover), Hoge (Minimus), Kyalla
(Muriel) , Sangartatta (Mollie) Barde
(Pinkeye) , Burtu (Moses), Dafale
(Bluebell), Durwa (Jessie), ‘Yarbaka
(Pitcher) da dai sauransu. Dabbobin
gandu dai sunci nasarar tawaye ne da
Karin karfin gwuiwar Wakar Dabbobin
Rugu wadda ke dumamasu :
Dabbobin rugu duk ku
saurareni
Dabbobin ko ina ku saurareni,
Nazo da zance mai faranta rai
Nan gaba ba wuya, idan mun
niyya
Lalle muna iya ture Dan Adam.
Daga nan sai kasa ta zanto
tamu
Mune muke iko da ko ina…
Shafi name 9
Sunan gandu ya canza daga Gandun
Nomau zuwa Gandun Dabbobi, har sun
tsara dokokinsu wadanda zasu yi
amfani dasu. Ga alamu dai, Dantulu
shugaba ne nagari mai hazaka da son
ci gaban dabbobi – ‘‘Ya ‘yan’uwana,
mu nufi saura, mu maida himmar
yankan tattaka, mu ga munfi Nomau
da barorinsa maida hankali Shafi na 18.
An fara samun banbancin zaman
gandu, da nuna fifiko da son kai tun
lokacin da aka fara tatsar madara ana
mallakawa aladu kawai, harda
nunannen mangwaro ma sai aladu
kawai ke moriyarsa. A duk lokacin da
sauran dabbobi suka fara guna-guni,
sai a tura musu Karambana don yayi
musu bayani. Saboda baiwarsa ta iya
magana, Karambana zai iya canza
baki zuwa fari. Yakan ce: Ya
‘yan’uwana, ina fatar zaku lura fa da
cewar mu aladu, ba muna yin haka ne
don nuna fifiko ko son kai. Da yawa
daga cikinmu ba mu son madara ko
mangwaro. Ni kaina bani kaunarsu.
Dalilin da yassa kawai muke shansu
shine don mu tsare lafiyarmu. Madara
da mangwaro, Ya yan uwana, ilimin
kimiya ya tabbatar da amfaninsu ga
aladu. Mu aladu, masu aikin tunani ne
kawai, dukkan shirye-shirye da
sarrafar da aikin gandun nan ya
dogara ne fa a kanmu. Dare da rana fa
tsaye muke don jin dadin ku kawai.
Saboda ku ne muke shan madara da
mangwaron nan. Shin me kuke zato
idan muka kasa yin aikinmu yadda ya
kamata? Nomau sai ya dawo… cikinmu
babu wanda yake son yaga Nomau ya
dawo. Shafi na 26.
Hassada da babakeren Maitumbi sunsa
yayi kulla-kullar korar Dantulu a
gandu, saboda babu jituwa a
tsakaninsu, duk lokacin da daya yacce
wannan ‘fari’ ne sai dayan yace a’a,
‘baki’ ne. Haka sunka saba yi har anka
iso ga muhawarar ginin famfo
(windmill) . Jim kadan da korar
Dantulu, sai ga aladu sun fara karya
dokokin gandu:
Duk abu mai kafa biyu abokin gaba ne
Duk abu mai kafa hudu, ko fuffuke,
dan’uwanmu ne
Kada dabbar da ta kuskura ta sa tufafi
Kada dabbar da ta kushura ta kwanta
kan gado [da barguna]
Kada dabbar da ta kuskura ta sha giya
[har ta bugu]
Kada dabbar da ta kuskura ta kashe
‘yar’uwarta [babu dalili]
Duk dabbobi darajarsu daya [amma
wasu sun dara wasu]
Dabbobi sun koma da cewa mulkin
Nomau yafi mulkin aladu dadi, ba
wa