Black Panther Fim ne na shekarar alif 2022 na kasar Amurka wanda ya dogara da kungiyar fina finai ta Marvel Comics wanda ke nuna halin Shuri / Black Panther. Kamfanin Marvel Studios ne ya samar da shi kuma Walt Disney Studios Motion Pictures ya rarraba shi, shine mabiyi na Black Panther (2018) da kuma fim na 30 a cikin Marvel Cinematic Universe (MCU). Ryan Coogler ya ba da umarni, wanda ya rubuta fim din tare da Joe Robert Cole, tauraruwar fim din Letitia Wright a matsayin Shuri / Black Panther, tare da Lupita Nyong'o, Danai Gurira, Winston Duke, Florence Kasumba, Dominique Thorne, Michaela Coel, Mabel Cadena , Tenoch Huerta Mejía, Martin Freeman, Julia Louis-Dreyfus, da Angela Bassett. A cikin fim din, shugabannin Wakanda sun yi yaki don kare al'ummarsu sakamakon mutuwar Sarkinsu T'Challa.