Etighi rawar Najeriya ce. Mutanen Akwa Ibom ne suka kafa wannan rawar etighi. Rawar tana buƙatar motsi na ƙafa da ƙugu. Rawar dai ta shahara a faɗin Najeriya kuma mutanen Ibibio da Efik ne ke amfani da salon rawar, inda anan ne rawar ta soma.[1]
Shahara
An yi amfani da raye-rayen salon rawar a cikin bidiyon waka da yawa a Najeriya da ma duniya baki-ɗaya. Rawar ta shahara ne a lokacin da mawaƙi Iyanya, ya yi amfani da rawan a cikin fitaccen bidiyon wakarsa.[2][3]
Manazarta