El Ard el Tayeba (laƙabi: The Kyakyawar Ƙasa ko Duniya mai Kyau, Larabci: الأرض الطيبة, fassara. Al-Ard Al-Tayyiba)[1][2][3] fim ne na Masar da aka shirya shi a shekara ta 1954, wanda Mahmoud Zulfikar ya rubuta kuma ya shirya shi.[4][5][6][7]
Takaitaccen bayani
Sa’adiya ta gano cewa ‘yar wani attajiri ce kuma tana da gado mai tarin yawa bayan rasuwarsa. Mahaifiyarta Baheega ta tsaneta, musamman bayan Sa'adiya ta zama mai arziki. Baheega ta kulla makarkashiyar kashe Sa'adiya don cin gadonta tare da taimakon masoyinta da ɗan uwanta. Anan wani mutumin kirki ya zo ya kubutar da ita.