Edward Percy Masha ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya taɓa rike muƙamin kwamishinan albarkatun ruwa a jihar Kaduna a zamanin gwamnatin Ahmed Mohammed Makarfi. A watan Satumbar 2024 ne aka zaɓe shi a matsayin sabon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Kaduna. [1][2][3]