David Nnaji ya kasance dan wasan fim din Najeriya ne, jarumi kuma marubuci, ya shahara saboda fitarsa a matsayin Ifeanyi a cikin television series Dear Mother.[1]
Farkon rayuwa da karatu
An haifi Nnaji a watan Yulin shekara ta alif ɗari tara da tamanin da biyar 1985 a Jihar Lagos, Najeriya kuma ya yi dukkanin karatunsa ne a jihar. Ya yi karatun digiri a fannin tarihi da tsare-tsare daga Jami'ar Lagos.[2]
Rayuwarsa
Nnaji shi ne na hudu daga cikin su biyar a wurin mahaifinsu, kuma yana da yara biyu, Chinualumogu Naetochukwu Nnaji da Adaezeh Munachimso Nnaji.[3]
Aiki
Bayan ya gama jami'ar Nnaji, Nnaji ya kafa kamfanin DUN Entertainment Limited. Ya riƙe matsayin Ifeanyi a cikin series Dear Mother wanda aka riƙa nunawa a televijin na kusan shekaru goma[yaushe?].[4]