Clive Needle (an haife shi ranar 22 ga watan Satumban, 1956) a Romford, Essex. tsohon ɗan siyasa ne na Jam'iyyar Labour a Burtaniya. Ya kasance ɗan Majalisa a Tarayyar Turai (MEP) na mazaɓar Norfolk daga shekarar 1994 zuwa 1999.
Farkon rayuwa da Karatu
An haife shi a Romford, Needled yayi karatu a Makarantar Sakandare ta Southend sannan a Jami'ar Aston. Ya zama mai shirya jam'iyyar Labour a Norfolk, kuma ya yi aiki a matsayin mai ba al'umma shawara.[1]
Fagen Siyasa
Takara
Bayan tsayawa takara da yin amfani da taken yakin neman zabe, "Be sharp - ku zabi Needel!",[2] An zaɓi Needle a matsayin MEP don Norfolk a cikin 1994, ta doke ɗan takarar Conservative Paul Howell na wa'adi uku, ɗa ga Ralph Howell ɗan majalisar Conservative na Arewacin Norfolk wanda ke cikin mazabar Norfolk Turai. Ya sake tsayawa takara a zaben 1999 sannan a shekara ta 2004 inda bai samu nasara ba, ya tsaya takara a mazabar Gabashin Ingila.[3]
Mulki
A lokacin mulki sa a Majalisar Tarayyar Turai, Needle ya kasance memba na kwamitin raya kasa da hadin gwiwa sannan kuma daga baya kwamitin kula da muhalli, lafiyar jama'a, da kare lafiyar masu amfani. Ya kuma zama mataimakin shugaban tawagar kan hulda da Transcaucasus.[4]
Rayuwa bayan Majalisar Turai
Needle ya zamo Babban Mashawarcin Siyasa ga EuroHealthNet, ƙungiya mai zaman kanta da ke inganta daidaiton lafiya a Turai.[5]
Iyali
Yana zaune na dan wasu lokuta a Brussels da kuma wani bangare a Ingila tare da iyalinsa.
Manzarta
- ↑ BBC-Vacher's Biographical Guide 1996. London: BBC Political Research Unit and Vacher's Publications. 1996. pp. 6–28. ISBN 0951520857.
- ↑ "Archived copy". Archived from the original on 1 November 2007. Retrieved 18 January 2008.
- ↑ "Archived copy". Archived from the original on 8 September 2005. Retrieved 18 January 2008.
- ↑ "Clive John Needle". European Parliament MEPs. Retrieved 4 August 2015.
- ↑ "Clive Needle". www.eurohealthnet.eu. Retrieved 4 August 2015.