Charles Uzo Azubuike lauya ne kuma ɗan siyasa a Najeriya. Ya taɓa zama mamba mai wakiltar mazaɓar Obingwa ta yamma a majalisar dokokin jihar Abia. An naɗa shi mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Abia daga shekarun 2007 zuwa 2011. [1][2][3] Ya taɓa zama mamba mai wakiltar Aba ta Arewa/Aba ta Kudu a majalisar wakilan Najeriya a majalisar wakilai ta 7 daga shekarun 2011 zuwa 2015 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP [4][5][2]
Azubuike ya yi karatun firamare da sakandare a jihar Abia. Ya halarci Jami'ar Jihar Abia (ABSU), inda ya samu digirin farko a fannin shari'a. [6]
Aikin siyasa
Uzo Azubuike ya riƙe muƙamai da dama a tsawon rayuwarsa ta siyasa. Ya kasance ɗan majalisar dokokin jihar Abia, ya wakilci mazaɓar Obingwa ta yamma, ya zama mataimakin kakakin majalisa, a majalisar dokokin jihar Abia daga shekarun 2007 zuwa 2011. [2][6] Ya kasance ɗan majalisar wakilai daga shekarun 2011 zuwa 2015. An zaɓe shi don wakiltar mazaɓar tarayya ta Obingwa/Osisioma/Ugwunagbo. [4] Gwamna Okezie Ikpeazu ya naɗa shi kwamishinan noma na jihar Abia, inda ya yi aiki daga shekarun 2015 zuwa 2017. [7]