Laftanar-Janar Charles Kayonga (an haife shi a shekarar 1962) sojan kasar Rwanda ne kuma jami'in diflomasiyya mai ritaya, wanda ya kasance, har zuwa 2019, Jakadan Rwanda a kasar Sin. [1][2] Ya taba zama Babban Hafsan Tsaro. Ya halarci Jami'ar Makerere a birnin Kampala, Uganda inda ya sami digiri na farko a fannin fasaha. Ya kammala karatu daga makarantar Rundunar Sojojin Amurka da Kwalejin Janar na Ma'aikata a Fort Leavenworth, Kansas. [3] A lokacin yakin basasar kasar Ruwanda, Kayonga ya rike mukaman soja daban-daban kuma mmuhimman abubuwan da ya yi fice a fannin aikinsa sun hada da cewa ya yi aiki a wurare daban-daban kuma ya kai mmatsayi daga Kwamandan Platoon zuwa Bataliya. Ya auri Caroline Rwivanga kuma yana da 'ya'ya 3. [4]