Bernard Udoh

Bernard Ambrose Udoh (an haife shi a ranar 16 ga watan Oktoba, 1962) ɗan siyasan Najeriya ne daga jihar Akwa Ibom. Ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Ikot Abasi/Mkpat-Enin/Gabashin Obolo daga shekarun 1999 zuwa 2003 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar People's Democratic Party (PDP). Akpan Micah Umoh ne ya gaje shi. [1] [2] [3]

Manazarta

  1. "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2025-01-05.
  2. Adeolu (2017-02-22). "UDOH, Hon. Bernard Ambrose". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 2025-01-05.
  3. "The Current Members of The Federal House of Representative from Akwa Ibom State". Uruan Community (in Turanci). 2010-02-09. Retrieved 2025-01-05.