Bengaluru ko Bangalore birni ne, da ke a jihar Karnataka, a ƙasar Indiya. Shi ne babban birnin jihar Karnataka. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2011, jimilar mutane miliyan sha biyu. An gina birnin Bengaluru a karni na sha shida bayan haifuwan annabi Issa.