Asibitin Koyarwa na Aminu Kano Asibitin Koyarwar Gwamnatin Tarayya ne dake cikin jihar Kano, Nigeria . An san shi da farko asibitin koyarwa na Jami'ar Bayero. Babban daraktan kula da lafiya na yanzu shine Abdurahaman Abba Shehe.
Ana amfani dashi don horar da ɗaliban likitanci na Jami'ar Bayero dake Kano, da likitanci na gaba (Horar da zama). Ya samu nasarori cikin shekaru gami da kasancewa asibitin gwamnati na farko da ya yi nasarar dashen koda a shekara ta 2002 kuma tsohon Babban Daraktan Likita Farfesa Abdulhamid Isa Dutse shi ne abin taimaka wa dashen. [1][2][3][4][5][6][7][8]