Anna Paulson (mai wasan ƙwallon ƙafa) |
---|
Rayuwa |
---|
Haihuwa |
Umeå (en) , 29 ga Faburairu, 1984 (40 shekaru) |
---|
ƙasa |
Sweden |
---|
Sana'a |
---|
Sana'a |
ɗan wasan ƙwallon ƙafa |
---|
|
|
Muƙami ko ƙwarewa |
fullback (en) |
---|
Lamban wasa |
93 |
---|
Tsayi |
1.69 m |
---|
Anna Sofia Perpetua Paulsson (an haife ta a ranar 29 ga watan Fabrairun shekara ta 1984) tsohuwar ƴar wasan kwallon kafa ce ta ƙasar Sweden. A lokacin aikinta ta taka leda a matsayin mai tsaron gida ga Umeå IK da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Sweden. Paulson ta fara bugawa tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa a ranar 10 ga Fabrairu na shekarar 2004 a kan Finland inda suka buga 1-1.
Ayyuka
Tun lokacin da ta fara bugawa Umeå a shekara ta 2001, Paulson ta kasance wani ɓangare ne na tsaron ƙungiyar. A cikin shekaru 10 da ta yi tare da Umeå, sun lashe Super Cup guda ɗaya, Kofin Mata na UEFA guda biyu, Kofin Sweden guda huɗu, da lambobin zinare biyar na gasar zakarun ƙasar Sweden.
A shekara ta 2011 Umeå ta ba Paulson ƙwangilar farfaɗo wa don tabbatar da lafiyarta, amma ta yi sake da damar ta a lokacin kakar. Wata kotun daga baya ta yanke hukuncin cewa sun karya kwangilar kuma sun ba Paulson 138,000 kronor.[1]
Manazarta
Hanyoyin Haɗin waje