An haifi Alexander a ranar 26 ga Maris 1980, kuma ya fito daga Ampomah-Kintampo ta Kudu a yankin Bono Gabas na Ghana. Ya yi SSSCE a shekarar 1999. Ya kuma yi BSc. a Ilimin Noma a 2012.[1]
Aiki
Alexander shi ne shugaban gundumar a ma'aikatar kananan hukumomi da raya karkara na gundumar Kintampo ta Kudu.[2][3][4]
Aikin siyasa
Alexander dan jam'iyyar NPP ne kuma a halin yanzu dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kintampo ta kudu.[1][5]
Kwamitoci
Alexander memba ne na kwamitin tabbatar da gwamnati kuma mamba ne a kwamitin sadarwa.[6]
Tallafawa
A cikin Nuwamba 2021, Alexander ya ba da abinci da sufuri kyauta ga ɗalibai kusan 1357 waɗanda suka kasance ƴan takarar BECE a mazabar Kintampo ta Kudu.[7]
Rigima
A watan Oktoba 2020 lokacin yana DCE na gundumar Kintampo ta Kudu, ya ba mahaifinsa lambar yabo a matsayin 'mafi kyawun manomi' a gundumar. A cewar Mathew Atanga, jami’in sadarwa na NDC ya yi ikirarin cewa an yi wa wasu manoman da suka cancanta fashi a wata sanarwa.[8]