Ahmed Douhou, (an haife shi ranar 14 ga watan Disamba na shikara 1976, a Bouake) ɗan wasan tseren Faransa ne wanda ya ƙware a tseren mita 200. Ya sauya sheka daga kasarsa ta haihuwa Cote d'Ivoire a shekara ta 2002. [1]
Ya lashe lambar tagulla a tseren mita 4x400 a gasar cin kofin Turai ta shekarar 2002, tare da abokan wasan Leslie Djhone, Naman Keïta da Ibrahima Wade. A mataki na mutum daya ya kai wasan kusa da na karshe na gasar cikin gida ta shekarar 1997 IAAF, kuma ya halarci gasar Olympics ta lokacin zafi a shekarun 2000 da 2004.
Kafin ya koma Faransa ya taimaka wajen kafa tarihin Cote d'Ivoire a tseren mita 4x100 na dakika 38.60, ya samu tare da abokan wasansa Ibrahim Meité, Yves Sonan da Eric Pacome N'Dri a Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2001 a Edmonton. [2]