Shaikh Abdulwahab Abdullah fitaccen Malami ne na addinin musulunci mazaunin garin Kano a Najeriya.
Farkon Rayuwa
Shaikh Abdulwahab Abdullah, An haife shi ne a ranar 28 ga watan Agusta na shekarar alif dari tara da hamsin da uku 1953, wanda ya yi dai dai da ranar Juma’a 17 ga watan Zul-Hijjah shekara ta alif dari uku da saba'in da uku 1373 Miladiyya, a ƙasar Togo.[1]
Karatu
Shaikh Abdulwahab Abdullah Ya soma karatu a wurin yayan mahaifinsa mai suna Imam Alhaji Yahya. Daga bisani ya yi karatu a wurin babban malami marigayi Imam Ɗan’ammu da ke birnin Kano. Kazalika ya kuma yi karatu a wurin Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Shehu Maihula da gidan Shamsu inda akwai malamai irin su Malam Gali, da Malam Babba.[2]
Zuwa Saudiyya
Bayan karutunsa a jihar Kano Najeriya, daga nan ne ya tafi Saudiyya tare da matarsa inda ya yi karatu a can. Malam ya yi karatu a wurin Sheikh Bn Bazz da Sheikh Uthaimin, waɗanda ya ce ya koyi halaye na gari da matuƙar tsoron Allah a wurinsu.[3]