A Deal with a Woman (Larabci: صفقة مع امرأة wanda aka fassara a matsayin Safqa Maa Imraa) wani fim ne na Masar da aka fitar a ranar 11 ga watan Fabrairu, 1985. Adel El Aassar ne ya ba da umarni a fim ɗin kuma taurarin fim ɗin sune Madiha Kamel, Hussein Fahmy, da Adel Adham.[1]
Takaitaccen bayani
Najwa, matar wani hamshakin attajiri, ce tana halartar zaman jinya tare da wani likitan mahaukata mai suna Sherif, wanda ke da takardar shaidar digiri na jabu daga Essam, wanda kuma yake amfani da shi wajen bata masa suna. Essam da Najwa sun kulla makarkashiyar kashe mijinta tare da kafa Sherif. Sherif yana jin yadda ta furta a cikin jinya cewa ta boye gawar mijinta bayan ta kashe shi. Najwa ta kamu da son Sherif, tana mamakin kishin Essam.[2]